Ina sa ran za mu lashe Premier League na bana – Arteta

Mikel Arteta ya ce ya kara jin cewar Arsenal za ta lashe Premier League na bana, duk da rashin nasara a hannun Manchester City.

Ranar Laraba, City ta je Emirates ta doke Gunners 3-1 a kwantan wasan Premier League karawar mako na 12.

Wadanda suka ci wa City kwallaye sun hada da Kevin de Bruyne da Jack Grealish da kuma Erling Haaland.

Kwallo na 26 da Haaland ya zura a raga a bana a Premier, yayi kan-kan-kan da yawan na Sergio Aguero a kungiyar a kakar 2014/15.

Gunners ta zare daya ne ta hannun Bukayo Saka.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta biyun teburi da makinta 51 iri daya da na City, wadda ta ba ta tazarar rarar kwallaye.

”Yan wasa suna da tabbacin za su lashe kofin bana, suna jin za su iya,” in ji Arteta.

City ce ta fitar Arsenal daga FA Cup a kakar nan, sannan Arsenal ba ya kai bante ba a Carabao da za buga wasan karshe tsakanin Man United da Newcastle.

Bayan da Gunners ta ci Manchester United a Premier ranar 22 ga watan Janairu, Arsenal mai kwantan wasa ta bayar da tazarar maki biyar.

Sai dai kungiyar ta ci karo da koma baya, wadda ta samu maki daya daga taran da ya kamata ta hada.

Ta yi rashin nasara a hannun Everton da 1-1 da Brentford ranar Asabar a Emirates.

Leave a Reply