“Ina Fargabar Fuskantar Barazana A Rayuwa Ta”- Dan Jaridar Da Ya Bankado Asirin Jami’o’in Ketare Masu Bada Shaidar Bogi

Dan jaridar da ya gabatar da binciken kwakkwafi kan wasu jami’o’in kasashen ketare da ke bayar da takardun kammala karatu na bogi, Umar Audu, ya bayyana damuwar sa kan yadda yace akwai yiwuwar ya fuskanci barazana ga lafiya ko rayuwar sa daga wadanda binciken sa bai yi musu dadi ba.

Umar Audu, wanda ke aiki da jaridar ‘Daily Nigerian’, ya mallaki takardar shaidar kammala karatun digiri cikin makonni shida, bayan da ya tsallaka zuwa daya daga cikin jami’o’in da ke kasashen ketare wadanda ake zargin suna bayar da shaidun bogi, har ma ya shiga sansanin horas da masu yi wa kasa hidima.

Da yake hira da gidan talabijin na Channels, Umar Audu yace a tsorace yake da irin halin da tsaro yake ciki a Najeriya, musamman ma wajen baiwa ‘yan jarida damar gudanar da yyukan su ba tare da shakku ba.

Sai dai yace duk da har yanzu bai ci karo da wata barazana ba, ya nesanta kansa daga cikin al’umma, domin samar wa da kansa tsaro da kwanciyar hankali.

Leave a Reply