Imran Khan na samun sauƙi bayan harin birnin Waziribad a Kasar Pakistan.

Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan na samun sauki a asibiti bayan an harbe shi a ƙafa yayin zanga-zanga a jiya Alhamis.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya rasa ransa yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka bayan da wani harbin bindiga ya daki motar da Mista Khan ke ciki a gabashin birnin Wazirabad.

Magoya bayansa sun dinga bin tituna a faɗin biranen ƙasar bayan harin da aka kai masa.

Tuni gwamnatin kasar ta yi Allah-wadai da waɗanda suka kai harin.

Amurka ,Birtaniya , Canada da Saudiyya na cikin kasashen da su ma suka yi tir da harin da ake ganin yunkuri ne na kashe Mista Khan ɗin.

Leave a Reply