ICPC ta sanar da kwato na’urar satar bayanai ta wayar tarho a gidan El-Rufai da ke Abuja

Hukumar yaki da cin hanci ta (ICPC) ta sanar da kwato wasu kayan aiki da ake zargin za a iya amfani dashi wajen sauraron tattaunawar wayar tarho a gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufaida ke Abuja.

Hukumar ta ce ta samu umarnin Kotun Majistare da ke Bwari a Babban Birnin Tarayya (FCT) domin tsare el-Rufai na tsawon kwanaki 14, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar Alhamis.

Haka kuma, hukumar ta roƙi Babbar Kotun Bwari dake Abuja da ta yi watsi da ƙarar da el-Rufai ya shigar, wadda ke zargin tauye masa ’yancinsa na ɗan Adam.

ICPC ta ce tsohon gwamnan na da zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya kamata ya amsa, ciki har da tambayoyi kan inda Yuro miliyan daya da dubu 400 suka shiga; da kuma tura wasu kuɗi zuwa asusun da ba a bayyana ba har N428,122,180.18, da sauransu.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa wani mataimaki na tsohon gwamnan, wanda ake zargin yana da alaƙa da lamarin, ya fice daga ƙasar.

Hukumar ta ce dukkan kayan da ake zargi, an kwato su ne a gaban matar tsohon gwamnan, Hadiza Isma el-Rufai, da ɗansa, Hon. Bello el-Rufai.

ICPC ta kuma zargi tsohon gwamnan da ƙin ba da haɗin kai ga masu bincike, inda ta ce ya zaɓi yin shiru har sai an kai shi gaban kotu. Ta ƙara da cewa wani mataimaki da ke da alaƙa da binciken ya tsere daga ƙasar.

  • Related Posts

    Ɗan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Adamawa

    Adamu Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa na Kwamishinan Ayyuka da Makamashi na Jihar Adamawa. A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan…

    Hukumar tsaro ta DSS ta murƙushe kungiyar safarar makamai a Gombe, Ta kwato rokoki

    Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta sanar  cewa jami’anta sun murƙushe wata ƙungiyar da ake zargi da safarar makamai a Jihar Gombe, tare da kama mutane biyu da ake…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ɗan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Adamawa

    Ɗan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Adamawa

    ICPC ta sanar da kwato na’urar satar bayanai ta wayar tarho a gidan El-Rufai da ke Abuja

    ICPC ta sanar da kwato na’urar satar bayanai ta wayar tarho a gidan El-Rufai da ke Abuja

    Hukumar tsaro ta DSS ta murƙushe kungiyar safarar makamai a Gombe, Ta kwato rokoki

    Hukumar tsaro ta DSS ta murƙushe kungiyar safarar makamai a Gombe, Ta kwato rokoki

    The Art of Crafting High-Quality Radio Content

    The Art of Crafting High-Quality Radio Content

    How We Keep Our Listeners Informed and Entertained

    How We Keep Our Listeners Informed and Entertained

    Exploring the Diverse Genres of Guarantee Radio FM

    Exploring the Diverse Genres of Guarantee Radio FM