Hunturu: Adadin waɗanda suka mutu na ci gaba da ƙaruwa a Amurka

Jami’ai a Amurka suna ce tsananin hunturu da ke ratsa arewacin Amurka na ci gaba da sanadin mutuwar mutane a jihar New York da ke Amurka.

Shugaban gundumar Erie Mark Poloncarz ya ce akalla mutum 34 ne suka mutu a gundumar ciki har da birnin Buffalo.

Tsananin sanyi tare da dusar ƙanƙara da ke sauka a faɗin Amurka tun lokacin hutun Kirsimeti a ƙarshen makon da ya gabata ya yi sandin mutuwar akalla mutum 60 a jihohin ƙasar takwas.

Gundumar Erie ce aka fi samun yawan waɗanda suka mutu a ‘yan kwanakin nan.

To amma an fara samun sauƙin yanayin a wasu jihohin ƙasar ciki har da New York.

Leave a Reply