Hukumar Zabe INEC Ta Yi Wa Jami’anta Sama Da Dubu 5000 Karin Girma

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi wa jami’anta 5,196 karin girma.

Hukumar ta sanar da haka ne cikin sanarwar da take fitarwa a kullum, wadda daraktar wayar da kan masu kada kuri’a Mrs Adenike Tadese ta fitar a babban birnin tarayya Abuja.

Tadese tace an dauki matakin daga likkafar tasu ne biyo bayan jarrabawar karin girma da hukumar tayi a karshen shekarar 2023, a wani yunkuri na ganin ta kyautatawa jami’anta tare da samar musu da cigaba a rayuwar su.

Kazalika hukumar ta bawa wasu daraktocin ta hudu umarnin tafiya hutun karshen shekarar da muke bankwana da ita.

Leave a Reply