Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta gayyaci Ganduje a kan ‘bidiyon dala

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aika takardar gayyata tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a kan ‘bidiyon dala’.

Wata sanarwa da hukumar ta PCACC ta fitar ta ce ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum da ake zargin cewa Ganduje ne lokacin da yake karɓar damin daloli yana zuba wa aljihu.

Sanarwar ta ambato Muhyi yana cewa: “Na sa hannu a kan wata wasiƙa don gayyatar shi ya zo a yi masa tambayoyi a hukumar cikin makon gobe, saboda abin da doka ta ce kenan kuma za mu bayar da ɗumbin damammaki don ya kare kansa”.

Sai dai, Mallam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano kuma makusancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu ba su samu takardar gayyatar da ake cewa hukumar ta aika wa tsohon gwamnan ba.

Kuma dangane da sahihancin bidiyon da hukumar Muhyi take iƙirari, Muhd Garba ya ce ba za su ce uffan a kan wannan batu ba, don kuwa magana ce da take gaban kotu.

Umar Abdullahi Ganduje dai ya sha musanta zargin, inda ya riƙa iƙirarin cewa abokan adawa ne suka shirya maƙarƙashiya da nufin hana masa damar shiga zaɓen 2019.

Lamarin dai ya janyo matuƙar ce-ce-ku-ce ba ma a Kano ba, har ma a Najeriya gaba ɗaya, abin da ya kai har majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin bincika gaskiyar lamarin.

Sanarwar dai ta ce hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano ƙarƙashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta nuna aniyar gudanar da bincike tun sa’ar da bidiyon ya bayyana, sai dai a lokacin Ganduje yana da rigar kariya a matsayinsa na gwamna.

Ya ce amma bayan komawarsa shugabancin hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen a ‘yan makwannin da suka wuce, sun yanke shawarar sake buɗe binciken don kuwa a cewarsa yanzu Gandujen ba shi da rigar kariya.

Muhyi Magaji ya ce zuwan Abdullahi Ganduje gaban hukumar don wanke kansa ko akasin haka, abu ne mai fa’ida saboda “bidiyon na ci gaba da janyo wa jihar da ma ‘yan jihar muzantawa a faɗin duniya”.

Leave a Reply