HUKUMAR NEMA TA KWASO ‘YAN NIGIRIA 105 DA SUKA MAKALE A KASAR CHADI

      Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA tace ta karbi ‘yan Najeriya mutum 105 da suka makale a kasar Chadi, bayan kwaso daga N’djamena babban Birnin kasar zuwa Babban filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano dake  nan Birnin Kano.

Babban jam’in shiyya na hukumar Dr Nuradeen Abdullahi, shine ya sanar da hakan lokacin da yake tarbar wadanda aka dawo dasu din anan Kano.

Yace an kwaso su matafiyan kyauta ne karkashin shirin hukumar kula da kaurar baki ta majalisar dinkin duniya IOM.

Wadanda hukumar ta karba sun hadar da maza 24 da mata 23 sai kuma kananan yara mata 33 da maza 25 wadanda suka fito daga jihohin Katsina, Kano Adamawa, Borno,  da kuma jihar Taraba da dai sauransu.

Leave a Reply