Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 919 Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi A 2023

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Katsina, ta ce jami’an ta sun samu nasarar kama haramtattun kwayoyi na sama da kilogram 500, tare da cafke mutane 919 da take zargi a shekarar 2023 da muke bankwana da ita.

Kwamandan hukumar na jihar ta Katsina, Hassan Sani Abubakar, shi ne ya bayyana samun wannan nasara, inda yace cikin mutanen da suka kama, 894 daga cikin su maza ne yayin da 25 kuma suke mata.

Kazalika ya koka kan karuwar samun tu’ammali da miyagun kwayoyi a Katsina, yana mai cewa jihar ta kasance ta biyu bayan Kaduna a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da aka fi samun yawaitar muguwar ta’adar.

Hassan Sani Abubakar ya kuma yi kira ga daukacin hukumomi da masu ruwa da tsaki, da su hada kai wajen yin aiki tare, domin kawo karshen tu’ammali da miyagun kwayoyi a jihar Katsina da ma Najeriya baki daya.

Leave a Reply