Hukumar kula da shige da fice ta Kasa ta sanarda fara bada fasfo na tsawon shekaru 10, a ranar 25 ga watannan inda za’a fara gwajin daga jihar Legas.
Mai magana da yawun hukumar Sunday James, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Ya kara da cewa, hukumar zata rufe shafinta na bada fasfo da ake amfani da shi tun da fari, domin a baiwa al’umma damar neman Fasfon a saukake.
Wannan mataki na sabunta zangon amfani Fasfo na tawon shekaru 10, na daga cikin manufofin shugaba Muhd Buhari, na inganta harkar shige da fice a Kasarnan.