Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Najeriya ta kori ma’aikatan ta guda biyu

Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta kasa ta kori ma’aikatan ta guda biyu, tare da daukar tsauraran matakaikan wasu 35 da ta samu da aikata laifuka daban daban.

Wannnan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawu hukumar na kasa Abubakar Umar ya fitar, inda yace an dauki matakan ne domin tabbatar da tsaftace aikin nasu, ta hanyar aiwatar da shi a kan tsari.

Jami’in yace wadanda aka dauki matakan a kansu, an same su da laifukan da suka hadar da sakaci da aiki, sata, shigar da abubuwan da aka haramta cikin gidajen, hada baki da kuma taimakawa masu laifi da dai sauran su, wanda ya bayyana su a matsayin barazana ga tsaro da ma zaman lafiyar al’umma.

Daga bisani y ace a bisa umarnin babban kwanturola na hukumar n kasa Haliru Nababa, zasu cigaba da zakulo masu kokarin bata musu aiki, tare kuma da kyautatawa wadanda suka nuna kwazo.

Leave a Reply