Hukumar Kula Da Aikin Dan Sanda Ta Najeriya Ta Bukaci A Gyara Aikin ‘Yan Sandan Sarauniya

Shugaban hukumar kula da aikin ‘yan sandan Najeriya Solomon Arase, ya bukaci a dauki matakan da zasu tsaftace aikin dan sanda musamman ma ta bangaren ‘yan sandan sarauniya da ake kira Constabulary a turance.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya fitar.

Arase yace daga cikin matakan, akwai bukatar a tantance wasu daga cikin su, da samar musu da nasu kalar kayan, ko ma a ruguje aikin nasu baki daya, sakamakon yadda yace suna sajewa cikin ‘yan sanda su kuma gudanar da abin da ya saba wa ka’idar aikin dan sanda, ciki har da cin zarafi, wanda yace hakan yana bata aikin a idon ‘yan kasa.

Ya kara da cewa hukumar za ta yi aiki da shugabannin rundunar ‘yan sandan Najeriya, wajen magance wannan matsala da kuma tsaftace aikin baki daya.

Leave a Reply