Hukumar Kidaya Za Ta Yi Amfani Da Hanyoyin Zamani Wajen Gudanar Da Aikin Kidayar Bana

Hukumar kidaya ta Najeriya tace za ta yi amfani da hanyoyin zamani wajen gudanar da aikin kidayar bana.

Kwamishinan hukumar reshen babban birnin tarayya Abuja, Hon. Joseph Shazin, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Abuja, yace za a yi amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen tattarawa tare da adana bayanan kowane dan Najeriya.

Kwamishinan dai ya kai wa kungiyar ziyara ne domin cigaba da gudanar da shirye shiryen aikin kidayar bana, da kuma wayar da kan al’ummar Fulani kan aikin.

Yace sun dauki wannan matakin ne domin kaucewa irin kalubalen da suka fuskanta a baya na rashin samun hadin kai, da kuma shan wahala kafin kaiwa ga al’ummar fulanin.

Leave a Reply