Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano zata fara karbar kudin ajiya na aikin hajji

Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano zata fara karbar naira miliyan Daya da dubu dari biyar, a matsayin kudin ajiya kafin Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da ainihin kudin kujerar hajjin shekara mai zuwa.

Hakazalika Hukumar tace  daga ranar Litinin zata fara mayarwa da maniyyatan da basu samu damar zuwa aikin hajji ba na 2022 da kudadensu.

Babban Sakataren Hukumar Ambasada Muhammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema Labarai a yau Litinin.

Yace dukkan wadanda suka ajiye kudadensu amma suka kasa cikawa suma zasu je ofishin Hukumar domin karbar kudaden na su daga ranar Litinin mai zuwa.

Ambasada Muhammad Abba Danbatta, ya kuma ce sun kammala tattara dukkan bayanai domin karbar kudaden abincin Alhazai na kwanaki hudu da ba a basu ba a kasa mai tsariki daga hannun hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON domin rabawa alhazan da suka cancanci hakan.

Leave a Reply