Hukumar ICPC Ta Hada Hannu Da Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Don Yakar Ayyukan Rashawa

Shugaban hukumar yaki da ayyukan rashawa ta Najeriya Dakta Musa Aliyu, ya bayyana cewa hukumar ta hada hannu da cibiyar kula da da’ar ma’aikata wajen gudanar da ayyuka tare.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ICPC Azuka Ogugua ta fitar a Abuja, inda tace an dauki matakin ne domin ganin an kawar da duk wani nau’i na ayyukan rashawa a fadin Najeriya, musamman ma a tsarin aikin al’umma.

Kazalika matakin hadin gwiwar na zuwa ne bayan da shugaban hukumar ICPC tare da mukarraban sa, suka kai ziyara ga ofishin mukaddashin shugaban cibiyar da’ar ma’aikatan, Aliyu Kankia a birnin tarayya Abuja.

Aliyu Kankia yace wannan wani yunkuri ne na tallafawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu wajen ganin an yaki ayyukan rashawa yadda ya dace, sakamakon hukumar da’ar ma’aikata ta kasance mafi karfi da kuma tasiri wajen yakar irin wadannan ayyuka a Najeriya, kamar yadda yake a kundin tsarin mulki da aka yiwa kwaskwarima na shekarar 1999.

Leave a Reply