Hukumar FRSC  ta kafa kotun tafi da gidan dan hukunta masu karya dokokin tuki.

Mukaddashin babban kwamadandan hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa FRSC Dauda Biu, ya bayar da umarnin kafa kotunan tafi da gidanka a jihohin kasar nan, ciki kuwa harda  Akwa-Ibom da yan jihar ke gwada karya dokokin tuki a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara.

Ya bayar da umarnin ne yayin fara wani kewayen rangadi na musamma na wata-wata don fadakar da direbobi, wanda ya gudana a karamar hukumar Ikot Ekpene dake jihar ta Akwa Ibom.

Dauda Biu, wanda ya samu wakilcin Ekette Bassey, ya roki ofisoshin hukumar FRSC dake yankin da su bada muhimmiyar kulawa akan harkokin zirga zirgar ababen hawa dan tabbatar da ganin an makala na’urorin rage guda a motocin haya da hana lodawa mata kaya fiye da kima.

Leave a Reply