Hukumar EFCC Ta Zargi Bankuna Da Hannu A Laifukan Harkokin Kudi A Najeriya

Hukumar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta zargi bankuna da daukar kaso 70 na yawan laifukan da suka shafi harkokin kudi da ake aikatawa a Najeriya.

Shugaban hukumar ta EFCC Ola Olukayode shi ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan lamuran tattara bayanan bankuna, inda ya bayyana wannan gudunmawa ta bankunan a matsayin abin da ke matukar ci musu tuwo a kwarya.

Kazalika yace masu amfani da bankuna wajen aikata laifukan kudi kullum karuwa yake, wanda ke bukatar a dauki mataki cikin gaggawa.

Olukayode wanda ya samu wakilcin daraktan sashen tattara bayanai na hukumar ta EFCC Idowu Apejoye, ya ce akwai bukatar kara sanya ido a bangaren daga sauran hukumomi, da masana masu ruwa da tsaki domin a dakile wannan barazana da suke fuskanta.

Leave a Reply