Hukumar EFCC Ta Fito Da Sabbin Ka’idojin Yin Kame Da Bayar Da Beli

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta sabunta ka’idojin yin kame da kuma bayar da beli kan wadanda take tuhuma da aikata laifuka.

Hukumar ta sanar da cewa daga yanzu za ta bayar da muhimmanci game da hakkokin wadanda take kamawa da kuma matakan ba da belinsu.

Shugaban hukumar Mista Ola Olukoyede ne ya ba da wannan umarni cikin sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce matakin ya shafi dukkan reshen hukumar da ke fadin Najeriya.

Kazalika, sanarwar ta ce daga yanzu dole a yi taka tsantsan wajen bukatar fasfo na kasa da kasa daga wurin wanda ake tuhuma, kuma hakan ya danganta da yanayin tuhumar da ake yi masa da yanayin mutumin da kasar da yake zama,.

Ya kara da cewa, dole ne a dakatar da ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma ba tare da wani kwakkwaran dalili na tsawon lokuta da suka wuce tanadin tsarin mulkin kasa.

An kuma gargadi jami’an hukumar kan take hakkin wadanda ake tuhuma ba tare da wata hujja ba.

Leave a Reply