Hukumar DSS Ta Musanta Janye Tuhumar da Take Wa Tukur Mamu a Kotu

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahoton da ke yawo cewa ta janye ƙarar da ta shigar da Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakani da ‘yan ta’adda.

Wani rahoton da ake yaɗawa ya yi ikirarin cewa hukumar ta janye ƙarar da ta shigar a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, inda ta samu sahalewar tsare shi na kwanaki 60.

Rahoton ya nuna Lauyan DSS, A. M Danlami ya shaida wa Mai shari’a Nkeonye Maha, jim kaɗan bayan kiran ƙarar, cewa hukumar ta jingine shari’ar.

Amma a wata hira da jaridar Daily Trust tayi da mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya musanta waccan rahoto.

Mista Afunanya ya jaddada cewa DSS ba ta janye ko tuhuma ɗaya da take wa Tukur Mamu ba, inda ya bayyana cewa lamarin wani batu ne da za’a ci gaba da gudanar da bincike akai.

Leave a Reply