Hukumar Da Ke Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa Ta Cafke Godwin Emiefele
Hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta cafke tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emiefele.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ta cafke tsohon gwamnan ne sa’o’i kalilan bayan da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta sake shi a daren Alhamis, inda tayi awon gaba da shi zuwa shelkwatar ta dake Jabi a babban birnin tarayya Abuja, domin ya amsa tambayoyi.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa akwai zarge zarge da dama da hukumar ke yiwa Emefiele, da suka hada da rashin tafiyar da aikin sa yadda ya dace a lokacin da yake kan kujera, kazalika akwai yiwuwar a tuhume shi da sabbin zarge zarge.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu damar ji daga bakin mai magana da yawun hukumar na EFCC kan wannan batu ba.