Hukumar Civil defense ta shawarci iyaye dasu kauracewa bada ‘ya’yansu aikatau.

Hukumar tsaron al’umma ta Civil defense ta shawarci iyaye dasu kauracewa bada ‘ya’yansu aikatau domin kaucewa cin zarafin yaran da kuma daukar munanan dabi’u.

Mai Magana da yawun hukumar reshen jihar Jigawa CSC Adamu Shehu, shi ne ya bayyana hakan a yayin da hukumar ta yi holan wasu mutum biyu da ta cafke bisa zargin safarar kananan yara zuwa birane domin aikin aikatau.

Ya ce mutanen sun fito ne daga kananan hukumomin Gwiwa da Ronin Jihar Jigawa, da ake zarginsu da safarar wata yarinya da suka rabata da iyayenta zuwa birnin tarayya Abuja.

CSC Adamu Shehu, ya kara da cewa da zarar sun kammala bincike zasu mika su ga kotu domin su girbi abin da suka aikata.

Leave a Reply