Hukumar Civil Defence Ta Kama Mutane 11 Kan Zargin su Da Aikata Laifuka Da Dama A Kano

Hukumar tsaron al’umma da muhimman kadarorin gwamnati ta kasa reshen jihar Kano tace ta samu nasarar kama mutane 11 da ake zargin su da aikata laifuka daban daban a fadin jihar.

Wannan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar na Kano SC Ibrahim Abdullahi a lokacin da hukumar ke holen wadanda aka kama, inda yace an kama su ne a unguwannin “Yan barka da Limawa dake yankin karamar hukumar Kumbotso a ranar 27 ga watan da muke ciki na Fabarairu.

Jami’in ya kara da cewa sun kuma samu nasarar cafke wani matashi dan shekaru 26 a karamar hukumar Doguwa, wanda ake zargin sa da tu’ammali da miyagun kwayoyi.

Ibrahim Abdullahi yace da zarar bincike ya kammala za su mika duk wadanda ake zargi izuwa kotu domin yanke musu hukunci, inda ya jadadda kudurin hukumar na ganin ta kare al’umma da kuma duk wasu muhimman kadarorin gwamnatin domin samar da cigaba a fadin jihar Kano.

Leave a Reply