A wani hoaon bidiyo da TVC NEWS ta wallafa, yanuna sojan karara tana watsawa ‘yar hidimar kasar ruwa mai datti.
Tuni dai rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa kuma ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a birnin Calabar na jihar Cross River, sannan ta yi Alla-wadai da ɗabi’ar sojar wadda rundunar ta ce ta saɓa wa dokokinta na kyawawan dabi’u.
Haka kuma rundunar ta ce ta ƙaddamar da bincike kan lamarin kuma an ɗauki mataki kan sojar sannan za a hukunta ta yadda ya dace.
Sannan ta bai wa matar mai yi wa ƙasa hidimar haƙuri kan tozarta ta da aka yi.