Sojojin da ke karkashin rundunar Operation Enduring Peace sun fara wani shiri na tsaurara bincike da sintiri a fadin birnin Jos, a jihar Plateau.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Captain Chinonso Polycarp Oteh ya fitar a ranar Asabar, ya ce an fara wannan aiki ne tun ranar Juma’a da ta gabata.
Ya ce matakin na daga cikin kokarin dawo da cikakken zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Plateau.
Sanarwar ta ce karin jami’an tsaro da aka tura sun fara samun nasara, inda sojoji suka kama wasu mutane biyu da ake zargi, tare da kwato bindigar AK-47 da harsasai guda hudu na da kuma wata karamar bindigar.
An gudanar da wadannan samame ne a wasu wurare masu muhimmanci a Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, ciki har da Dadinkowa, Old Airport Junction, Tudun Wada da kuma unguwar Low-cost.


