Harin bam ya kashe ɗan sanda a Pakistan

Aƙalla ɗan sanda ɗaya ne ya mutu tare da raunata mutane da yawa sakamakon wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai a birnin Islamabad na Pakistan a yau Juma’a.

Kafar talabijin ta Geo News ta ruwaito Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Sohail Zafar Chattha na cewa ɗan sandan ya ceci birnin baki dayansa.

“Ɗan sandan ya ceci birnin Islamabad daga mummunan bala’i ta hanyar ƙarfin hali da kuma kulawa,” in ji shugaban ‘yan sandan.

Ministan Harkokin Cikin Gida Rana Sanaullah ta ce maharin ya so ya kai hari ne kan wani “muhimmin wuri”.

“Da maharin ya cimma manufarsa da ya zama abin kunya ga ƙasarmu,” a cewar ministar.

Rahotanni sun ce mutum huɗu ne suka jikkata a harin da aka kai a cikin mota.

Leave a Reply