Hankalin Ronaldo ya rabu, Man Utd na tattaunawa kan Gakpo

Cristiano Ronaldo, ya samu tayi daga kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya wadda za ta  ba shi kudin da ya kai fam miliyan 150 a shekara, bayan rabuwarsa da Manchester United.

Dan wasan na Portugal na dab da cimma yarjejeniya da kungiyar ta Saudi Arabia.

Sai dai kuma ana ganin tauraron na Portugal har yanzu yana son taka leda a gasar Zakarun Turai saboda haka har yanzu bai yanke shawara kan ansar wannan tayi ba.

Manchester United na tattaunawa da wakilan dan gaban PSV Eindhoven Cody Gakpo kan sayen dan wasan na Netherlands a watan Janairu.
Watakila matashin dan wasan tsakiya na Brighton Billy Gilmour dan Scotland ya tafi Villarreal aro a watan Janair

Leave a Reply