Gwanatin jihar kano ta sanar da sallamar ma’aikata hudu dake aiki a ma’aikatar kula da tsara birane ta jihar wato KNUPDA bayan kama ma’aikatan da laifi sayar da filaye ba bisa ka’ida ba, amfani da takardin bogi lokacin sayar da filayen, bayar da bayanan bogi da sauran laifuka.
Ma’aikatar yada labarai karkashin jagorancin Comrd. Muhammad Garba ce ta fitar da wannan sanarwa bayan kammala binciken da akayi akan korarrun ma’aikatan duba da yadda korafe korafe suka yi yawa a kan su tare da kama su da laifin da ake zargin su dashi.