
Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shi ne ya sanar da hakan bayan ziyarar da ya kai Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar, inda ’yan gudun hijirar da suka tsere daga Najeriya ke zama.
Gwamna Tambuwal, ya ce za su gudanar da taron ne tare da gwamnonin jihohin Dosso, Tahwa da kuma Maradi na Jamhuriyar Nijar.
Daga cikin gwamnonin Najeriya da za su halarci taron har da takwarorinsa na jihohin Kaduna, Zamfara dakuma jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana cewa abun takaici ne yadda matsalar rashin tsaro ta dabaibaye yankin nasu, duk kuwa da cewa suna yin iya bakin kokarinsu don samar da zaman lafiya.
ya kuma mika sakon godiyar Shugaban kasarnan Muhammadu Buhari ga Shugaba Mohammed Bazoum, a kan karamcin da kasarsa ta yi wa Najeriya na kula da dubban ’yan gudun hijirar da suka samu matsuguni a Nijar.