Gwamnonin arewacin Najeriya na taron gaggawa a yau Litinin a Kaduna domin tattauna batutuwan da suka danganci harajin VAT.
Rahotanni na cewa gwamnan Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ne zai karbi bankwancin taron wanda shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong zai jagoranta.
Taron na zuwa ne bayan ministan shari’a a Najeriya, Abubakar Malami ya shaida cewa babu wata jiha da ke da ikon karbar harajin kasa.
Batun bai wa jihohin damar karban harajinsu kamar yadda wasu jihohin kudu da suka hada da Legas da Rivers ke ta fafutika ya haifar da ce-ce-ku-ce da ci gaba da jan hankula ‘yan Najeriya.
A watan da ya gabata wata kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta yanke hukunci cewa jihar Rivers na da damar karban kudaden harajinta.
Sai dai hukumar tattara kudaden haraji ta Najeriya, FIRS, ta daukaka kara ta na mai kalubalantar hukuncin.