Kungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriya ta yi watsi da matsayin takwarorinsu na kudanci da ke cewa sai lallai shugaban kasar na gaba ya fito daga kudancin Najeriya.
A lokacin wani taro da kungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta yi jiya a Litinin, ta ce babu wanda zai tilasta wa yankin zaɓen shugaban kasa daga wani sashen kasar.
Matsayar gwamnonin na zuwa ne bayan a watan Yuli kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun bukaci alatilas a basu dama mulki ya koma garesu domin tabbatar da adalci.
Sannan gwamnonin Arewar na cewa matsayar takwarorinsu na kudanci kan harajin VAT alamace da ke nuna sun daburce wajen gane bambanci harajin VAT da wanda ake daurawa lokacin cinikayya.
Masana harkokin siyasa dai na cewa wannan dambarwa alama ce da ke nuna bangarorin biyu sun ja layi a tsakaninsu.