Gwamnatin Zamfara ta gargadi al’umma da suyi taka-tsantsan da sansanin da mayakan ISWAP suka bude a jihar.

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa mayakan ISWAP masu ikrarin jihadi a yammacin Afirka, sun kafa wani sansani a kauyen  Muutu na gundumar  Mada, dake karamar hukumar Gusau a Jihar.

Shugaban kwamitin bincike da bibiyar ayyukan ‘yan fashin daji da sauran laifuffuka a jihar Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, shi ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da ya gudana a Gusau, babban birnin jihar.

Ya kuma ce ‘yan kungiyar ta ISWAP sun shiga jihar ne ta kauyukan Danjibga-Kunchin Kalgo dake Karamar hukumar Tsafe, inda ya ci gaba da cewa daruruwan ‘yan ta’addan sun tashi wasu garuruwa dake kusa da kauyukan a hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.

Ya ce Gwamnan Jihar Bello Matawalle, ya yi amfani da karfin ikon da doka ta bashi wajen rufe wasu kafafen yada labarai a jihar don tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply