Gwamnatin tarayya tace satar mai ke kara kawo rashin aikin yi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yawaitar satar danyen mai da ake yi na da alaka da rashin aikin yi a kasar nan.

Ministan samar da ayyukan yi Dr. Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin taron majalisar dake kula da daukar ma’aikata wanda aka gudanar a Abuja karo na takwas.

Chris Ngige, wanda shi ne shugaban majalisar ya kuma bayyana cewa wannan satar man da ake yi na kara durkusar da tattalin arzikin kasar nan, inda ya kara da cewa hakan na dakushe kokarin gwamnati na samar da ayyukan ga ‘yan kasa musamman matasa.

Leave a Reply