Gwamnatin tarayya tace Rohoton sakamakon da aka fitar ya nuni da cewa ana samun wadanda miciji kan saraa kasar nan daga daga Mutum dubu 15 zuwa dubu 20 a kowacce shekara.
Karamin ministan lafiya na kasa Dr. Olorunnimbe Adeleke Mamora, shine ya bayyana hakan a wajen wani taron manaima labarai da ma aikatar ta shirya don bikin zagayowar ranar wayar da kan al umma hanyoyin gujewa cizon miciji.
Dr Mamora yace jihohin da aka fi samun matsalar ta cizon miciji sune Gombe, Plateau, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Benue da kuma Taraba.
Dagan an sai yayi kira da akara rubanya kokari wajen hada hannu guri guda da wadannan jihohi domin kawar da wannan matsala ta cizon miciji a jihohin su baki daya.