Gwamnatin Tarayya Tace Biyan Kudin Haraji Zai Taimaka Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurin ta na habaka tattalin arzikin Najeriya da akalla kaso 18 nan da shekaru 3 masu zuwa, ta hanyar tabbatar da cewa ‘yan kasar na biyan kudaden haraji ga hukumomi masu alhaki.

Shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta Najeriya Dakta Zacch Adedeji shi ne ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi wajen taron kara wa juna sani da kungiyar masu bada rahoto kan kasuwanci da ayyukan kamfanoni ta shirya, inda yace hakan zai yi matukar taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Dakta Adedeji, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar reshen jihar Legas, Mrs. Fadekemi Oyeniyi, ya nuna irin muhimmiyar rawar da kudin haraji yake takawa a tattalin arzikin kowace kasa, yana mai cewa yana taimakawa gwamnati wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta na ganin ta biyawa ‘yan kasa bukatun su.

Leave a Reply