Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa Tsarin Ciyar Da Daliban Makaranta Naira Biliyan 100 A Kasafin Bana

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa an ware wa tsarin ciyar da daliban makaranta Naira Biliyan 100 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 da muke ciki.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake sanya wa kasafin kudin hannu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace hakan zai matukar taimakawa wajen kara wa al’umma karfin gwiwar sanya ‘ya’yan su a makaranta, tare da rage yawan yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba.

Idan dai za a iya tunawa a watan Disambar shekarar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya sake bullo da tsarin ciyarwa a makarantu, inda ya bayar da umarnin a mayar da shi karkashin kulawar ma’aikatar ilimi daga ma’aikatar jin kai.

Kazalika shugaban ya jaddada cewa kasafin shekarar nan, zai zama wani tsani da gwamnatin sa za ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wahalhalun da ‘yan Najeriya suke fuskanta.

Leave a Reply