Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Farfado Da Fannin Ilimi A Najeriya

Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ya amshi taswirar yadda za’a farfado da sha’anin ilimi don magance matsalolin da ake fuskanta a fannin, inda ya kuma yi alkawarin cewa za su dauki duk matakan da suka dace wajen inganta karatun firamare da sakandare har ma da na manyan makarantu.

Ministan wanda ya bayyana hakan a lokacin da mambobin kwamitin da ke karbar rahoton taswirar ilimi a Abuja suka kai masa bayani, yace a matsayin su na ‘yan Najeriya ba su ji dadi ba, saboda Najeriya ta kasa cimma abin da ya kamata a fannin, cikin shekaru uku da suka gabata.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Farfesa Nuhu Yakubu, ya ce an dora wa kwamitin alhakin duba batutuwan da suka shafi ingancin ilimi, inganta manhajoji, bayanan ilimi, tabbatar da kwarewa da bunkasa harkokin kasuwanci da koyo da dai sauransu.

Leave a Reply