Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Ranar Fara Neman Fasfo Ga ‘Yan Najeriya Ta Yanar Gizo

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, yace tsarin neman fasfo ta hanyar yanar gizo zai fara aiki daga ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2024.

A watan Disambar da ya gabata, ministan ya ce gwamnatin tarayya tana ci gaba da shirye shirye na ganin an fara amfani da tsarin cikin kankanin lokaci, inda a lokacin yace aikin ya kusa kammala, ya kuma kara da cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya su tanadi kananan hotuna da kuma duk wasu takardu masu muhimmanci.

Yayin da ya kai ziyara ga babban kwanturolan hukumar kula da shige da fice ta kasa a babban birnin tarayya Abuja, Ojo yayi wa ‘yan Najeriya albishirin cewa wahalar da suke fuskanta wajen samun fasfo ta zo karshe.

Leave a Reply