Gwamnatin Ondo ta umarci Dalibai da Ma’aikatan jihar da su koma yin shigar gargajiya a ranakun Juma’a.

A wani yunkuri na son bunkasa al’adun gargajiya a jihar Ondo, Gwamnatin jihar ta bayar da dama ga Ma’aikata da dalibai da suke sanya kayayyakin gargajiya wajen tafiya makarantu da wuraren aiki a ranakun juma a.

 

Kwamishinar yada labarai da wayar da kai ta jihar Uwargida Bamidele Ademola-Olateju, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Acewar ta daga yanzu gwamnatin jihar ta sahalewa duk wani ko ma aikaci da yayi shigar gargajiya wajen tafiya makaranta da wuraren aiki a duk ranar juma a.

Da yake jawabi kan wannan cigaba da aka samu kwamishinan raya al adu da yawon bude idanu Mista Adewale Akinlosotu, yayi bayanin cewa majalisar zartasar jihar taga dacewar baiwa ma aikatan gwamnatin jihar da dalibai damar yin shigar gargajiya ta Kabilar Yoruba wajen tafiya aiki da makarantu a duk ranar Juma a.

Leave a Reply