Gwamnatin Najeriya ta amince da hutun haihuwa na kwana 14 ga ma’aikata maza

Gwamnatin Najeriya ta amince a rinƙa bayar da hutun haihuwa na kwana 14 ga maza masu aikin gwamnati.

Shugabar ma’aikata ta gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce “gwamnati ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikata maza waɗanda matansu suka haihu na tsawon kwanakin aiki 14.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ba za a iya ɗaukar hutun fiye da sau ɗaya ba a cikin shekara biyu.

Haka nan za a iya ɗaukar hutun ne na haihuwa huɗu.

Article share tools

Leave a Reply