Gwamnatin Kogi ta buƙaci Basaraken jihar ya yi bayani kan rashin halartarsa taron Buhari

Gwamnatin jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta buƙacin sarkin Ebira Dakta Ado Ibrahim da ya yi ƙarin bayani kan zargin da take yi masa na rashin girmama shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Yahaya Bello.

Rahotonni na cewa gwamnatin jihar na zargin basaraken da rashin zuwa domin tarbar shugaban ƙasar a lokacin da ya kai ziyara jihar cikin watan Disamban da ya gabata.

A wata wasiƙa mai ɗauke da san hannun daraktan hukumar kula da masarautun gargajiya a jihar, an buƙaci basaraken da ya yi bayani a rubuce cikin kwana biyu”.

Haka kuma an buƙaci sarkin da ya bayyana a gaban wani kwamiti da gwamnatin jihar za ta kafa domin ya bayar da bahasin da zai gamsar da kwamitin daga ladabtar da shi”.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya halarci jihar domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Yahaya Bello ya gudanar.

Leave a Reply