Gwamnatin Kano zata dauki nauyin wanda suka kone sakamakon wutar da wani matashi ya kunna musu

Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin daukar matakin Shari’a, kan matashin nan mai suna Shafi’u Abubakar, da ake zargi da bankawa jama’a wuta a lokacin da suke yin sallar Asuba, a yankin Unguwar Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano, inda mutane 24 Suka kone sakamakon Iftila’in.
Gwamnan Abba Kabir, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, don duba wadanda Suka gamu da iftila’in konewar
Haka zalika gwamnatin jahar Kano, ta yi alkawarin daukar nauyin jinyar wadanda Suka gamu da iftila’in.
A Ranar Lahadin da ta gabata rundunar Yan Sandan jahar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 17 cikin 24 da Suka ga mu da iftila’in Kunar wutar.
Tawagar gwamnan Kanon da suka ziyarci majinyatan ajiya Lahadi , sun da Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, da kuma Darektan hukumar tsaron farin kaya DSS reshen jahar Kano, da kuma sauran mukarraban gwamnati.

Leave a Reply