Gwamnatin Kano ta jaddada kudirinta na samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari daga ketare

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa zata kulla yarjejeniya da masu zuba jari daga  kasar Sin, wajen samar da kamfanin sarrafa siminti a jihar Kano.

Darakta janar ta hukumar kula da zuba hannun jari ta jihar Kano Hajiya Hama Ali Aware ce ta bayyana hakan, a yayin da ta karbi bakuncin masu zuba hannun jarin kasar Sin da suka zo daga jamhuriyyar Nijar domin neman sahalewar gwamnati wajen kafa kamfanin siminti a jihar Kano.

Ta kuma bayyanawa ‘yan kasuwar cewa akwai damarmaki a zuba hannun jari a jahar Kano ta la’akari da tashar tsandauri ta Zawachiki, da matatar samar da makamashin iskar gas ta AKK dake Tamburawa da dai sauran ababen da zasu saukaka musu zuba hannun jari da gwamnatin jihar Kano ta samar karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Hama-Aware, ta kara da cewa jihar Kano a shirye take wajen ci gaba da karbar masu zuba hannun jari daga ko’ina a fadin duniya.

Tun da fari a nashi jawabin, shugaban tawagar Sinawan Mr. Ru Changyu, ya ce sun zo hukumar ne domin samun dukkanin goyon baya da hadin kai wajen kafa kamfanin sarrafa siminti a jihar Kano.

Leave a Reply