Gwamnatin kano ta cimma wata yarjejeniya da kasar Somalia a bangaren bunkasa harkokin noma da raya al’ada.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine ya jaddada wannan alkawari lokacin da yake karbar bakuncin Jakadan kasar Somalia a Najeriya Jamal Muhd Barru yayin wata ziyara ta musamman da ya kawowa gwamnan.
Ganduje yace jihar Kano da kasar Somalia suna musayar kasuwanci mai kamanceceniya da juna da kuma abinda ya shafi harkokin noma.
A jawabinsa Jakadan kasar Somalia a Najeriya Jamal Muhd Barru yace biyu daga cikin abubuwan da suka kawo shi kasar nan shine tsarin yadda shugabancinta yake da sauran abubuwabn da akasashen 2 suka bujiro da su domin inganta Mahallansu da habaka harkokin kasuwanci irin na kasa da kasa.
A wani cigaban labarin kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin wata tawaga daga kasar Faransa karkashin jagorancin Shugaban sahin kyautata huddar kasa da kasa Mista Pont wanda ya zo jihar nan domin kyautata kan fannin ilimi da bayar gurbin karatu kyauta domin karantar Ilimin kimiyya da Fasaha a kasar.
Da yake mayar da jawabi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da cigaba da kula da yarjejeniyar dake tsakanin bangarorin 2 wacce aka dakatar da ita tun a shekarar 2019 a sakamakon matsalar tattalin arziqi.