Gwamnatin Kano Ta Bawa Makarantar Kimiyya Da Fasaha Da Tashar Kano Line Wa’adin Tsaftace Muhallan Su

Gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Injinya Abba Kabir Yusif, ta bawa makarantar Kimiyya da Fasaha ta jihar da kuma tashar mota ta Kano Line wa’adin tsaftace muhallan su, ko ta dauki matakin da ya dace a kansu.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi na jihar Honorabul Nasiru Sule Garo shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai, jim kadan da kammala zagayen tsaftar muhalli na karshen wata wanda yake gudana a duk Juma’ar karshen wata da Asabar, inda yace akwai bukatar kowanne lokaci a dinga kula da muhalli don kare kai daga kamuwa da cututuka.

Shima a nasa bangaren shugaban kungiyar direbobin tifa na jihar Kano Ado Umar Santar Lungu, ya bayyana cewa za su cigaba da bawa gwamnatin gudumawar da ta dace, domin kawar da dukkanin sharar dake ciki da wajen kwaryar Kano.

Leave a Reply