Gwamnatin Kano Na Binciken Shugaban Gidan Talabijin Na ARTV

Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano,  ta ƙaddamar da bincike dangane da zargin almundahana kan Shugaban Gidan Talabijin na jihar ARTV, Alhaji Mustapha Adamu Indabawa.

Binciken na zuwa bayan ƙorafin da Ƙungiyar ’Yan Jarida NUJ da Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin suka gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ƙungiyoyin na zargin Alhaji Indabawa da almundahanar kuɗin da suka kai Naira miliyan ɗari da kuma saɓa ka’idar aiki.

Idan za a tuna dai Alhaji Indabawa na ɗaya daga cikin shugabannin hukumomi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a watannin baya bayan nan.

Duk laifukan da ake zargin Alhaji Indabawa sun ci karo da sashe na 26 na Kundin Dokokin hukumar PCACC kuma mafi ƙanƙantar hukuncin shi ne cin sarƙa ta shekara uku.

Leave a Reply