Gwamnatin Kaduna za ta tallafa wa ‘yan jihar don rage musu raɗaɗin ƙarancin kuɗi

Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa za ta tallafa wa ‘yan jihar domin rage musu raɗaɗin da suke ciki sakamakon ƙarancin takardun kuɗi.

Hakan ya biyo bayan wani zama na kwamitin tsaro da aka gudanar a jiya wanda gwamna Nasir El-Rufai ya jagoranta tare da hukumomin tsaro da aka aike jihar da sarakuna da kuma jami’an gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta ce batun ƙarancin kuɗin ya janyo wahalhalu da dama ga mazauna jihar sannan basa kuma iya biyan kuɗaɗe a bangaren sufuri da na kiwon lafiya da kuma sauran abubuwan yau da kullum musamman ma kayan abinci. A don haka, ta ce tallafin zai gudana har na tsawon mako ɗaya.

Gwamnatin ta ce za ta fito da wani tsarin sufuri da za a rinka ɗaukan mutane kyauta a biranen Kaduna da Zariya da kuma Kafanchan.

Ta kuma ce za a yi wannan tsari ne tare da haɗin gwiwar kungiyoyin sufuri da suka kunshi motocin bas da kuma a daidaita sahu

Leave a Reply