Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin da ake mata na tsige Sarkin Musulmi

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar Abubakar Bawa ya fitar a ranar Talatar nan, ta ce gwamnatin Ahmed Aliyu Sokoto ba tada wani shirin na tsige Mai Alfarma Muhammad Sa’ad, don haka ta yi Allah wadai da wannan zargi.

Tun a karshen makon da ya gaba ne rahotannin zargin tsige Mai Alfarma sarkin Musulmin, inda a martanin da  kungiyar kare hakkin Musulmi ta Najeriya MURIC ta fitar kan wannan lamari, ta ce bincikenta ya tabbatar da cewa gwamnan jihar Ahmed Aliyu na shirin mika takardar bukatar tsige sarkin Musulmin gaban majalisar dokokin jihar kowane lokaci daga yanzu.

Sakamakon wannan dambarwa, gwamnatin Najeriya ta gargadi gwamnatin jihar Sokoto game da zargin shirin tsige mai alfarma sarkin Musulmi

Leave a Reply