Gwamnatin Jihar Kano zata ayyana dokar ta baci kan fannin Ilimin Jihar baki daya

Gwamnan Jihar Kano, Enginner Abba Kabir Yusuf zai ayyana dokar ta baci kan ilimi a matsayin wani mataki na garanbawul a bangaren a fadin kananan hukumomin kano baki daya.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, yace wannan ya zama wani bangare na cika alkawarin da ya dauka a yayin da yake yakin neman zabe a shekarun baya da yayi.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce, sanarwar ta kuma yi daidai da shirin Gwamna na kara kaimi wajen inganta ayyukan ilimi da tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga daukacin mazauna yankin.
Gwamna Yusuf ya nuna matukar damuwarsa game da koma bayan ilimi a yankin, yana mai nuni da shirinsa na aiwatar da sauye-sauye a matakin manyan makarantun sakandare da firamare.

Leave a Reply