Gwamnatin jihar Kano ta ware kudi sama da naira miliyan 730 domin gina daki mai gadaje 52

Gwamnatin jihar Kano ta ware kudi sama da naira miliyan 730 domin gina daki mai gadaje 52 a asibitin kwararru na Muhd Buhari dake jihar Kano.

Aikin zai hada da samar da wajen kwanan ma’aikatan jinya da ofisoshi da wajen cin abinci da kuma bandakuna.

Wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamna Ganduje, Ameen Yassar ya fitar, tace yayin daya kai rangadi kan inda ake aikin, Ganduje yace aikin zai samar da karin gadaje ga majinyata musamman masu fama da ciwon daji da suke zuwa daga ciki da wajen jihar Kano.

Ganduje ya kara da cewa za’a kammala aikin nan da watanni hudu zuwa biyar tare da daga darajar asibitin.