Gwamnatin Jihar Kano ta shirya domin kawo cigaba a gidan talabijin na Abubakar Rimi

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa gwamnatin Kano a shirye take wajen kawo cigaba a gidan talabijin da rediyo na Abubakar Rimi, ta hanyar inganta kayayyakin aiki, domin a gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta hannun daraktan ayyuka na musamman na ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano, Sani Abba Yola, kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban girma da sabon Manajan Daraktan gidan talabijin din ya kai masa.

Dantiye, wanda ya taya sabon Daraktan murna, ya bayyana cewa, baya ga sayo kayan aiki na zamani ga gidan talabijin din, gwamnati za ta tabbatar da horar da ma’aikatan ta, tare da tabbatar da kulawa da su yadda ya kamata.

Tun da farko, sabon Manajan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi, Alhaji Mustapha Adamu Indabawa, ya bayyana cewa na’urorin da ake amfani da su a gidan sun tsufa kuma suna bukatar gyara.

Ya kuma nuna jin dadinsa da irin hadin kan da ya samu daga ma’aikatan tun bayan da ya kama aiki, ya kuma yi alkawarin bada gudunmawa wajen samar da ayyukan cigaba ga al’umma.

Leave a Reply